text
stringlengths
1
6.82k
aika wannan shafi facebook
aika wannan shafi email
aika wannan shafi whatsapp
aika wannan shafi
wannan shafukan na waje ne kuma za su bude ne a wani shafin daban
game da aika wa
rufe wurin aika labari
image caption jam'iyyar adawa ta pdp a najeriya
jam'iyyar adawa ta pdp a najeriya ta ce dirar mikiya da jami'an hukumar tsaro ta farin kayadss a kasar ke yi kan manyan alkalan kasar an dauko hanyar kashe dimukradiyyar kasar ce
cikin wata sanarwa da sakataren yada labaranta na kasa prince dayo adeyeye ya fitar jam'iyyar ta yi zargin cewa dirar mikiyar ta kara fito wa fili da salon kamakarya da gwamnatin muhammadu buhari ke yi
jam'iyyar ta ce a halin yanzu alkalai hudu ne da suka hada da sylvanus ngwuta da inyang okoro na kotun koli da kuma muazu pindiga da adeniyi ademolada na manyan kotu na ke tsare a hannun hukumar ta dss
jam'iyyar ta pdp ta ce da badan jajircewar da gwamnan jihar rivers nyesom wike ya yi ba da jami'an hukumar ta dss sun kama alkali na biyar mai shara'a abdullahi liman
a cikin sanarwar jam'iyyar ta pdp ta yi zargin cewa lokacin samamen jami'an hukumar ta dss sun ci zarafin alkalan sannan suka lakadawa wasu ma'aikatan gidajensu duka
ta kuma bayyana hakan a matsayin wani yunkuri na shugaba muhammadu buhari na mayar da bangaren shari'a 'dan amshin shata'
ta ce kamata yayi a bi hanyoyin da ya kamata idan ana zargin alkalan da aikata laifi ta hanyar aikewa ta takardun koke ga hukumar dake kula da ayyukan alkalai ta kasa
jam'iyyar pdp ta kuma bayyana wasu abubuwa da ta ce yi wa dokar najeriya karan tsaye ne da gwamnatin muhammadu buhari ke yi wadanda suka hada da yin dirar mikiya da jami'an dss suka yi a majalisun dokokin jihohin akwa ibom da zamfara da ci gaba da tsare mutane da dama duk da umurnin sakinsu da kotu ta bayar
ko a lokacin mukin kamakarya na sani abacha ba ayi wa ma'aikatan bangaren shari'a irin wannan dirar mikiya ba pdp ta ce
shugaba buhari ya nuna ba ya mutunta turakun demukradiyar kasar nan ya nuna ya na so ya kashe dimukradiyyar ya mayar da ita mulkin kamakarya jam'iyyar ta kara da cewa
jam'iyyar ta ce gwamnatin najeriyar ta ki ta mutunta umurnin kotun ecowas game da kanar sambo dssuki
pdp ta ce ya zama wajibi 'yan najeriya su yi magana don kare mulkin demukradiya daga lalacewa
a safiyar asabar ne hukumar ta dss ta ce ta gano makudan kudade a gidajen alkalan da ta kama
jami'an hukumar sun kaddamar da sumamen ne a babban birnin kasar abuja da port harcourt da gombe da kano da enugu da kuma sokoto
ku蓷a蓷en da aka samu a gidajen alkalai
hukumar dss ba ta kai samame ba da manufar keta hakkin bangaren shari'ar kasar ba
abdullahi garba mai magana da yawun dss
karin bayani
an dade dai ana zargin alkalan najeriya da cin hanci
ko makonni kimanin biyu da suka gabata sai da hukumar da ke sa ido kan harkokin shari'a a kasar ta kori wasu manyan alkalai bisa samun su da laifin cin hanci
nigeria yaki da cin hanci ya fara a bangaren shari'a
shin buhari zai iya magance cin hanci
an dai kori babban alkakin kotun jihar kano mai shari'a kabiru auta da babban alkalin kotun daukaka kara da ke zama a ilorin mai shari'a mohammed ladan tsamiya
da kuma babban alkalin kotun enugu mai shari'a i a umezulike
hukumar ta ce ta kori wasu daga cikin alkalan bisa karbar nagoro game da batutuwan da suka shafi zaben kasar na shekarar 2015
tun dai hawan mulkin kasar muhammadu buhari ya lashi takobin yaki da rashawa da cin hanci da suka yi wa kasar dabaibayi
tura wannan labarin game da aika wa
ka'idojin amfani
manufar tsare sirri
copyright 漏 2018 bbc bbc ba za ta dauki alhakin abin da ke kunshi a wasu shafukan na daban ba karanta tsarinmu game da bakin shafuka
'rafali ne ya ci mu' ferguson bbc news hausa
tsallaka zuwa abubuwan da ke ciki
abinda ke ciki
shiryeshirye na musamman
shiryeshiryen rediyo
aika wannan shafi facebook
aika wannan shafi email
aika wannan shafi whatsapp
aika wannan shafi
wannan shafukan na waje ne kuma za su bude ne a wani shafin daban
game da aika wa
rufe wurin aika labari
majan kulob din manchester united sir alex ferguson ya soki rafali lee mason saboda rashin soke cin da kulob din birmingham suka yi wa kulob dinsa a 'yan mintunan karshe na wasan da suka tashi daya da daya
ferguson ya ce kwallon ta taba hannun dan wasan birmingham kuma an yi wa rio ferdinand keta kafin a ci kwallon amma rafali ya kau da kai
shi ya sa muka ce wa hukumomin gasar premier su nemo rafali da zai iya ganin irin wadannan laifuka da 'yan wasa suke aikata wa a filin wasa in ji ferguson
kulob din na manchester dai da farko yana gaban birmingham da da ci dayan da dmitar berbatov ya jefa masa kafin daga bisani ana sauran 'yan mintuna a kare wasan lee bowyer na kulob din birmingham ya farke
tura wannan labarin game da aika wa
ka'idojin amfani
manufar tsare sirri
copyright 漏 2018 bbc bbc ba za ta dauki alhakin abin da ke kunshi a wasu shafukan na daban ba karanta tsarinmu game da bakin shafuka
nigeria majalisa ta juya wa buhari baya kan nadin magu bbc news hausa
tsallaka zuwa abubuwan da ke ciki
abinda ke ciki
shiryeshirye na musamman
shiryeshiryen rediyo
nigeria majalisa ta juya wa buhari baya kan nadin magu
aika wannan shafi facebook
aika wannan shafi email
aika wannan shafi whatsapp
aika wannan shafi
wannan shafukan na waje ne kuma za su bude ne a wani shafin daban
game da aika wa
rufe wurin aika labari
hakkin mallakar hoto femi adesina/ facebook
majalisar dattawan najeriya ta ki tabbatar da sunayen wadanda shugaban kasar muhammadu buhari ya nada a matsayin kwamishinonin hukumar zaben kasar inec
majalisar ta yi hakan ne a wani mataki na ramako ga bangaren zartarwar kasar kan ci gaban mukadashin shugaban hukumar yaki da cin hanci ta efcc da zama a kan kujerarsa bayan 'yan majalisar sun ki tabbatar da shi
zaman majalisar na ranar talata wanda shugabanta bukola saraki ya jagoranta ya dakatar da nazari kan sunayen kwamishinonin inec 27 din da buhari ya tura majalisar ne har sai bayan mako biyu
daga farko dai 'yan majalisar sun nemi hana majalisar magana kan tantance sunayen kwamishinonin ne gaba daya amman daga baya sanata saraki da mataimakinsa ike ekwerenmadu sun nemi 'yan majalisar su yi hakuri a dakatar da tantancewar na wucin gadi
bayan haka ne sanatan da ya gabatar da kudirin dakatar da tantancewar sanata peter nwaboshi da ke wakiltar delta ta arewa ya gyara kudirin nasa kuma majalisar ta amince da hakan
wasu daga cikin 'yan majalisar sun yi ikirarin cewar mukadashin shugaban hukumar efcc yana musu bitadakulli bayan sun ki tabbatar da shi a matsayin shugaban hukumar
nigeria zan yi ayitatakare da cin hanci da rashawa magu
nigeria shin saraki ya wawure naira biliyan 35
me ya sa buhari ya sake tura sunan magu majalisa
bukola saraki ban aikata laifin komai ba
a ranar ltinin ne dai kafafan yada labaran kasar suka byar da rahoton cewar ibrahim magu ya mika wa shugaban kasar muhammadu buhari wani rahoton da ke cewa shugaban majalisar dattawan bukola saraki ya wawushe naira biliyan 35 a cikin kudin lamunin paris club din da aka mayarwa najeriya
amman saraki ya musanta hakan yana mai cewar ramakon gayyan ne mukaddashin shugaban efcc ke yi don kin tabbatar da shi a kan mukaminsa
rahotanni dai sun ce an mika wa shugaba buhari rahoton na efcc ne ranar 10 ga watan maris inda majalisar dattawan kasar ta ki tabbatar da ibrahim magu a mukaminsa ranar 15 ga watan na maris
labarai masu alaka
cin hanci da rashawa
tura wannan labarin game da aika wa
ka'idojin amfani
manufar tsare sirri
copyright 漏 2018 bbc bbc ba za ta dauki alhakin abin da ke kunshi a wasu shafukan na daban ba karanta tsarinmu game da bakin shafuka
chadi ta mayar da 'yan gudun hijira 300 nigeria bbc news hausa
tsallaka zuwa abubuwan da ke ciki
abinda ke ciki
shiryeshirye na musamman
shiryeshiryen rediyo
chadi ta mayar da 'yan gudun hijira 300 nigeria